Najeriya: Darakta Janaral Ta Hukumar Yaki Da Safarar Mutane Najeriya Tace Za’a yi amfani Da Wasannin Motsa Jiki

NAPTIP
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Darakta janaral ta hukumar dake yaki da safarar mutane a Najeriya Julie Okah-Donli tace za’a yi amfani da wasannin motsa jiki wajen yaki da safarar mutane a kasa.

Okah-Donli ta bayyanawa manema labarai wan nan jawabin a gurin wasa na IBB Golf club yayin wasannin da aka shirya kan rannar yaki da fatucin mutane ta duniya na shekarar 2019.

Ta kara da cewa an gudanar da wasan ne don samar da hanyar wayar da kan mutane kan illar safarar mutane. San nan ta bayyana cewa hukumar zata hada gwiwa da masu ruwa da tsaki ciki har da masu shirya wasanni don a wayar da kan mutane.

Haka nan ta kirayi matasa da suke da sha’awar wasannin motsa jiki dasu bi ma’aikatan hukumar yayin tafiya kasashen waje don gudanar da wasannin motsa jiki.

Related stories

Leave a Reply