Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeriya: Buratai Ya Ziyarci Jami’ansa A Jihar Borno

Chief-of-Army-Staff-Major-General-T-Y-Buratai
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojin Najeriya karkashin Operation lafiya a jihar Borno sun samu karfin gwiwa bayan zuwan shugaban rundunar Laftanal janar Tukur Buratai.

Ya kai ziyarar ne bayan da yan ta’addan Boko Haram suka kai musu hari a kauyen Gasarwa dake kan titin Gajiram zuwa Monguno a karamar hukumar Nganzai dake jihar Borno.

Daraktan rikon kwarya, mai hulda da jama’a Col. Sagir Musa, ya bayyana cewa an hade jami’an Sector ta 3 karkashin Operation lafiya Dole zuwa Super Camp dake Monguno.

Ya kara da cewa masu zirga-zirgan sun hadu da yan ta’addan inda sukayi musayar wuta suka hallaka da dama wasu kadan suka tsere da raunuka.

A cewarsa jami’an sun samu makamai da dama daga hannun yan ta’addan, inda 3 daga ciki suka rasa rayukansu.

Buratai, ya halarci gurin da abun ya faru a Maiduguri ranar juma’a da rakiyar ragowar jami’an daga Hedikwatar. Inda daga baya ya wuce barikin Monguno inda ya gana da shugaban rundunar Operation Lafiya Dole da sauran shugaban nin.
Haka nan ya ziyarci asibitin da aka kwantar da jami’an da suka samu raunuka.

Related stories

Leave a Reply