Najeriya: Gwamnan Jihar Borno Ya Dau Alkawarin Kula Da Yan Bautar kasa

zulum
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Babagana Bukar Wakil, Maiduguri.

Gwamnan jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya farfesa Babagana Umara Zulum ya tabbatar da bada tsaro gay an bautar kasa da ake tura jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan bayan da ya karbi Darakta Janaral na hukumar ta NYSC Birgediya janaral Shuaibu Ibrahim da tawagarsa.

Zulum ya bayyana cewa sun zo ziyarar a dai-dai lokacin da jihar Borno ta fara farfadowa daga rikicin Boko Haram, san nan ya godewa yan bautar kasar da suka zo jihar inda yace zasu basu taimakon da ya dace.

San nan yaroki da a gudanar da horarwa nan gaba a Maiduguri, san nan a turo wadanda zasu taimaka wajen lafiya, kimiyya da fasaha.

Haka nan ya bukaci da atantance yan bautar kasar kuma a biya su kudadensu ta asusun bankunansu cikin sati.

Birgediya janaral Shuaibu Ibrahim ya godewa gwamnan da mutanen jihar Borno gaba daya.

Related stories

Leave a Reply