Najeriya: Buratai Ya Gana Da Jami’ansa A Maiduguri

By: Babagana Bukar Wakil

Shugaban hafsan sojojin Najeriya Laftanal janaral Tukur Yusufu Buratai ya halarci taron da jami’an suka gudanar a Command and Control Center dake Maiduguri a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ranar 26 ga watan Yuni na shekarar 2019.

Rahoton ya fito daga daraktan hulda da jama’a na rundunar kanal Sagir Musa, inda yace kimanin jami’an 300 ne suka halarci taron gada shiyyoyi daban daban inda suka samu zantawa ta musamman baki da baki da shugaban rundunar.

Taron an gudanar da shi ba tare da takura ba inda kowa ya bayyana abinda ke cikin ransa da abubuwan da suke damunsa ta bangaren ayyuka, kudadensu, gurin zama, da kuma cigaba da kalubale da ake samu.

Buratai ya yabawa jami’an kan yadda suke kokari da sadaukar da ransu wajen yaki da ta’adda a arewa maso gabashin Najeriya. Haka nan ya kiraye su dasu dinga bayyana masa matsalarsu don ya dauki mataki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *