Najeriya: Buhari Yayi Umarni Da Kar A Saurarawa ‘Yan Ta’adda Sakamakon Kisan Mutane 60 A Jihar Borno

buhari-talkingwidth-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yayi umarni da kar asaurarawa ‘yan ta’adda sakamakon kisan mutane sittin da sukayi yayin zaman makoki a jihar Borno.

Mai Magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu ne ya bayyana a rahoton da ya fitar a Abuja, inda yace shugaban kasar ya fada cewa ya samu tabbaci daga jami’an tsaro cewa zasu dauki kwakwaran mataki kan wadanda suka aikata wan nan aikin.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta dauki mataki kan kare martaba da tsaron kasar.
Haka nan Buhari na kan bakansa na cewa gwamnatinsa a shirye take ta kawo karshen ta’addanci a kasar, haka nan jami’an tsaron sama da kasa na nan na farautar wadanda suka gudanar da wa nan mumunan aikin.

San nan ya tabbatar wa mazauna Maiduguri da wadanda ke sansanin ‘yan gudun hijira cewa za’a kara basu tsaro na musamman kan kare wasu hare-haren.

‘Yan ta’addan sun kai hari kauyen Badu dake karamar hukumar Nganzai inda suka kashe mutane fiye da 60 suka jiwa 11 rauni.

Leave a Reply