Najeriya: Buhari Yayi Alkawarin Daukar Tsattsauran Matakai Kan Kisan Goronyo

buhari-talkingwidth-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin daukar tsattsauran matakai game da kisan gillar mutane talatin da bakwai da yan bindiga suka yi a karamar hukumar Goronyo dake jihar Sokoto.

Shugaban ya yi Allah wadai da wannan mummunar aika-aikara tare da jajantawa iyalen wadanda abin ya rutsa da su.

Wannan na cikin wata sanarwa da mashawarcin shugaban kasa na musamman akan yadda labarai Malam Garba Shehu ya bayyana, inda yace a halin yanzu an jibge jami’an tsaro a yankunan da suke fama da matsalar tsaro.

Shehun ya kuma ce fadar shugaban kasa da jihohi suna tattaunawa domin samar da masalaha da kuma samun al’ummar da abin ya shafa da nufin tattaunawa.

Related stories

Leave a Reply