
By: Zara Ngubdo
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yasa hannu kan kasafin kudin shekarar 2019 ranar Lahadi, masana sun bashi shawara kan a tabbatar anyi amfani da kudaden ta hanyoyin da suka dace.
Shugaban ya kirayi yan majalisun da kar suyi kokarin canza komai a kasafin kudin wanda hakan zai kawo matsaloli musamman kan farfadowar tattalin arziki.
Shugaban yasa hannun a ofishinsa dake fadar shugaban kasar a Abuja inda yace kasafin na yan majalisar a shekarar data gabata Naira tiriliyan 8.92 ne, wanda nashi Naira tiriliyan 8.83 lion inda nasun ya haura nashi da Naira biliyan 90 a kasafin da ya bayar ranar 19 ga watan Disamba na shekarar 2018.
Ya kara da cewa yan majalisar sun rage wasu ayyukan sun kara wasu ciki harda wasu saababbun ayyukan a kasafin kudin na bara.
Haka nan ya godewa yan majalisun kan kokarin da suke na ganin an mika kudirin kasafin kudin ina yace kasafin 2019 cigaban na bara ne wanda zai ciyar da kasar gaba.
Kan batun mika kasafin kudin ga shugaban yan majalisar wakilai Hon. Yakubu Dogara shugaban yace duk duniya babu inda ake cewa sai yan majalisa sun yarda da kasafin kudi.
Dogara ya bada amsa sakamakon rashin halartar taron da shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki akan lokaci sakamakon wasu ayyukan.
Ministan kasafi da tsare-tsare Sanata Udo Udoma ya bayyana kasafin a matsayin aikin hadin kai tsakanin gwamnati da yan majalisu.
