Najeriya: Buhari Ya Tabbatar Da Nadin Mohammed Adamu Matsayin Shugaban Yansanda

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar da nadin Mohammed Abubakar Adamu a matsayin shugaban yansanda na kasa.

Ya tabbatar da rahoton ne ranar Alhamis da rana a dakin taro na hukumar yansandan ta kasa dake babban birnin kasar Abuja.

A farko dai an nada Adamu a matsayin mai rukon kwarya ranar 15 ga watan junairu na shekarar 2019 bayan da ya karba daga tsohon shugaban yansandan Ibrahim Idris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *