Najeriya: Buhari Ya Nemi Taimakon Bankin IDB

President-Miuhammadu-Buhari-wide-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi taimakon bankin Islamic Development Bank (IDB) don cike wasu gurabe na ababen more rayuwa.

Mai Magana da yawun shugaban Femi Adesina ne ya bayyana hakan inda yace shugaban yayi kiran yayin taro da mataimakinsa da kuma shugaban Bankin Dr Mansur Muhtar a taron kungiyoyin Afrika da aka gudanar Niamey dake jamhuriyar Nijar.

Shugaban ya kara da cewa saboda yawan ‘yan kasar dole a samu karancin ababen more rayuwa, haka nan ba kananan kudade ne zasu habbaka kasar Najeriya ba.

San nan ya godewa IDB kan shiga harkar noma, kasuwanci da zuba jari, farfado da kauyuka, da samar da abinci ga kasar Najeriya inda yace idan suka kara taimako a kan wanda suke yi zai kawo karshen wasu matsalolin.

A ta bakinsa shugaban bankin Muhtar ya godewa Najeriya kan yarjejeniyar da kasashen Afrika kan cinikayya inda yace abubuwa zasu yiwa kasar kyau a yanzu da aka samu yarjejeniyar cinikayyar.

Related stories

Leave a Reply