Najeriya: Buhari Ya Nada Sabon Sakataren Hukumar NDLEA

president-muhammadu-buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mr Shadrach Haruna a matsayin sabon sakatare na hukumar hana fataucin miyagun kwayoyi.

Hakan na cikin wani rahoto da shugaban hukumar mai kula da hulda da jama’a Mr Jonah Achema.
Ya kara da cewa Haruna ne ya maye gurbin Mrs Roli George wadda wa’adin ta ya kare a watan Yuni na shekarar 2018.

Achema ya kara da cewa sakataren shugaba ne a sakatariyar inda yake kula da harkar jama’a, da kula da littattafai, tare-tsare da kuma yanke hukunci.

Haruna kwararre ne ta fannin shari’a kuma tsohon mai yanke hukunci ne wanda yayi aiki a ma’aikatar shari’a.

Related stories

Leave a Reply