
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai hada kwakkwaran kungiyar da zata samar da ayyuka da shirye-shirye a wan nan gwamnatin tasa.
Ya bayyana hakan a bikin ranar damokarariyya da aka gudanar a dandadlin Eagle Square dake Abuja ranar laraba 12 ga watan Yuni na shekarar 2019, haka nan shugaban bai bayyana yadda zai bada mukamai ba.
Buhari ya kara da cewa mulkin sa a karo na biyu zai bada karfi a kan cigaban da aka samu a shekara 4 na baya san nan a gyara kurakuran da aka samu.
