Najeriya: Buhari Ya Bada Umarnin Kawo Karshen Kiyayya Tsakanin Tiv Da Jukun

President-Miuhammadu-Buhari-wide-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari ya bawa gwamnati da sarakunan gargajiya na jihohin Benue da Taraba umarnin kawo karshen kiyayya tsakanin kabilun Tiv da Jukun.

ya bada wan nan umarnin ne bayan kisan wani babban malamin kirrista mai suna Rev. Fr. David Tanko a kauyen Kpankufu dake jihar Taraba.

Rahoton ya fito daga mataimaki na musammman kan harkar yada labarai da hulda da jama’a Mallam Garba Shehu, haka nan ya bada umarni da kabilun Tiv da Aku Uka dake wukari da suyi taron gaggawa na kawo karshen wadan nan rikice-rikicen.

Shugabn ya kara da cewa gwamnatin tarayya baza ta zauna tana kallon irin wan nan zamantakewar ba tsakanin kabilun Tiv da Jukun.

San nan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da jama’ar malamin kiristan, dagwamnatin jihar Taraba kan wan nan rashin da suka yi. .

Ya kara da cewa gwamnati zata tura jami’an tsaro yankunan don ganin an kawo karshen wadan nan rikice-rikicen. Karshe ya kirayi jama’a dasu bawa zaman lafiya muhalli.

Related stories

Leave a Reply