
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin sake daukar ma’aikatan yansanda dubu dari 4.
Shugaban sashin yada labarai na ma’aikatar yansandan Odutayo Oluseyi ne ya bayyana hakan a rahoton day a fitar inda yace hakan zai magance karancin ma’aikata a hukumar.
Ministan kula da harkar yansanda Mohammed Din gyadi ya kafa kwamitin mutane 13 don gudanar da aikin daukar ma’aikatan.
Mambobin kwamitin su fito da kyawawan ayyukan dasu ka kamata da tsarin aikin.
