Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeriya: Buhari Ya Amince Da Samar Da Jirage Masu Dauke Da Na’urar Daukar Hoto A Iyakokin Kasar

drone
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da samar da jirage masu dauke da na’urar daukar hoto da jirage a iyakokin kasar.

Majiyar ta bayyana cewa hakan na daga cikin matakan da jami’an fasa kauri zasu dauka na dakile shigo da kaya ba bisa ka’ida ba ciki harda safarar kaya da mutane.

Tuni dai aka kafa wai shiri mai suna “EX-SWIFT RESPONSE” don dakile wadan nan ayyukan.Shirin na Ex-SWIFT RESPONSE za’a dinga kula dashi ne daga ofishin shugaban mai bada shawara kan sha’anin tsaro na kasa da kuma hukumar yansanda, jami’an fasa kauri, jami’an shige da fice, sojoji da kuma ragowar jami’an tsaro.

Hami’an shige da fice sun bayyana cewa baza su bar duk wani da bashi da takardu ya tsallake iyakar ba. Haka nan sun bayyana cewa sun fitar da kimanin mutane 728 wadanda suka shigo ba bisa ka’ida ba.

Related stories

Leave a Reply