
Borno State Primary Health Care Development Agency da Nigeria State Health Investment Project zasu bada magunguna kyauta a sansanonin yan gudun hiijira a jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya.
Bankin duniya ne ya bada taimakon ta hanyar guraren shan magani matakin farko da manyan asibitoci dake a birnin, Maiduguri da garin Kaga.
Daraktan BOSPHCDA, Dr. Sule Meleh ne ya bayyana hakan a Maiduguri, yayin da yake ganawa da shugabannin shirin da kuma ma’aikatan lafiya yayin wani horo.
Ya bayyana cewa yan gudun hijirar na bukkatar kayan da kula dasu kamar su juna biyu, kayan haihuwa, kayan gwaji da maganin ciwon sida, maganin tazarar haihuwa da sauransu.
