
Akalla gidaje dari da kuma shaguna masu yawan gaske ne mayakan Boko Haram suka kona a harin baya-bayan nan da suka kai a ‘kauyukan Borri, kaleri-Abdulle da kuma Wanori dake wannan jiha.
Cikin wata sanarwa da mashawarcin gwamna na mussamman a kan hulda da jama’a Malam Isa Umar Gusau ya sanyawa hannu ya bayyana cewa shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jiha Hajiya Yabawa Kolo ita ce ta bada tabbacin faruwar lamarin ya yin da gwamna Umara Zulum ya ziyarci al’ummar da iftila’in ya rutsa da su.
Hakazalika YabawA Kolo ta kuma tabbatar da cewa gidaje 73 da kuma shaguna 28 a kauyuka uku na ‘karamar hukumar Konduga.

Al’ummomin da jafa’in ya rutsa da su suna rayuwa ne a yankin kudancin dajin Sambisa, sa’annan garin Konduga gari ne da ya yi fama da hare-haren mayakan Boko Haram cikin shekaru biyar da suka gabata.
Ya yin ziyarar gwamnan ya bayyana cewa ya ganewa idanuwansa kafin daga bisani ya gana da al’ummara da kuma shuwagabannin su. Bugu da kari ya kuma tattauna da matasa wadanda suke taimakawa ‘yan sa kai, ‘yan kato da gora wadanda suke taimakawa jami’an tsaro ya yin gudanar da ayyukan su.
