Najeriya: Babban Daraktan CSLAC Ya Soki Buhari Kan Bada Sunayen Mutanen Da Ake Zargi Da Cin Hanci Da Rashawa

Rafsanjani
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Babban darakta na kungiyar Civil Society Legislative Advocacy Centre, Auwal Ibrahim Musa Rafsanjani ya soki shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari kan saka sunayen mutanen da ake zargi da cin hanci da rashawa cikin sunayen ministoci da ya mika majalisar kasar.

Ya bayyana hakan a jamia’ar Bayero dake Kano yayin wata hira ta ‘yan jaridu, Rafsanjani ya soki shuagaban kan zabar mutanen da aka ce sun kwasi dukiyar kasa ba bisa ka’ida ba.

Duk da bai ambaci sunan shugaba Buhari ba da wadanda yake fada din ba, Rafsanjani ya kara da cewa yana mamakin yadda ake ganin Buharin zai nada irin wadan nan mutanen a gwamnatinsa.

Rafsanjani, dai shine sakatare janar mai rikon kwarya na kungiyar West Africa Civil Society wanda ‘yan jarida ke kira da Civil Society Organizations.

Haka nan babban editan Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ya bayyana amfanin kafafen yada labarai wajen yaki da cin hanci da rashawa, inda yace sai ‘yan jarida sun tashi tsaye sunyi yaki da cin hanci da rashawa ba tare da tsoro ko daga wani kafa ba kamar yadda ake a kashen da suka ci gaba.

Related stories

Leave a Reply