Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeriya: Ba Wata Barazana Da Yan Biafra Suka Yiwa Shugaba Buhari A Kasar Japan

femi-adesina-1
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Haramtarciyar kungiyar dake yunkurin kafa kasar Biafra bata samu yin barazana ga shugaba Muhammadu Buhari ba tunda ya isa garin Yokohama dake kasar Japan.

Rahoton ya fito daga mai bada shawara na musamman kan harkar yada labarai da hulda da jama’a Femi Adesina, inda yayi kira ga yan Najeriya dake gida da waje da suyi watsi da duk labaran da ake yadawa na cewa yan kungiyar sun yiwa shugaban kasa da yan tawagarsa bore da cewa kanzon kurege ne kawai.

Adesina ya kara da cewa suyi watsi da masu yada jita jita wanda basu gane cewa yan Najeriya basa tare dasu ba.
Haka nan ya kara da cewa Buhari zai halarci taron na 7 a taron duniya na Tokyo kan cigaban kasashen Afrika.

Related stories

Leave a Reply