Najeriya: Ba A Iya Kai Taimako Kananan Hukumomi 4 A Jihar Borno – UNICEF

UNICEF ta bayyana cewa ba’a iya zuwa a bada da taimako a kananan hukumomi 4 a jihar Borno dake Arewa maso gabashin najeriya sakamakon yan ta’addan dake yankunan.

Ta kara da cewa sakamakon yan ta’adda dake yankunan baza su iya kai taimakon gaggawa ga mata da yara dake yankunan ba. A satin da ya kamata ‘yan ta’addan sun kwace karamar hukumar Marte amma jami’an sojoji sun karyata hakan, Haka nan sun kira mai Magana da yawun rundunar wayar shi a kashe.

UNICEF ta bayyana cewa bayan Marte da suka kwace a satin da ya gabata akwai Abadam, Guzamala, and Kukawa wadanda kwata-kwata ba a iya zuwa sai Rann dake karamar hukumar Kala Balge wadda take da wahalar zuwa.

Sun kara dacewa da yawa daga cikin kananan hukumomin jihar ba a iya zuwa sosai saboda ana yawan samun hare-hare.
Haka nan hanyoyin basu da kyau shi yasa suke amfani da jirage masu saukar ungulu don su samu shiga wasu guraren don bada taimako ciki harda karamar hukumar Monguno inda yan gudun hijra kimanin 15,000 suka koma wata 6 da ya gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *