Najeriya: Atiku Yayi Kira Da Ayi Bincike Kan Gawar Da Akace Sojojin Na Binnewa Ba Tare Da Sanin Iyalansu Ba

Atiku
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a babban zaben da ya gabata, Atiku Abubakar yayi kira da a kafa kwakwaran kwamitin bincike Twanda kwararren mai shari’a da ba ruwansa da harkar siyasa zai shugabanta da a binciki zargin da akayi na binne gawar sojoji 1000 da ‘yan kungiyar Boko Haram suka hallaka.

Atiku, wanda tsohona mataimakin shugaban kasa ne ya bayyana cewa wan nan yunkuri na boye kisan sojojin abin kunya ne kuma kamata yayi dukkanin manyan kasar nan su dauki lamarin da mahimmanci domin gano gaskiyar lamarin.

Jawabin nasa na kunshe ne a wata sanarwa da ofishinsa na yada labarai ya fitar a garin Abuja. Atikun yace ‘yan najeriya nada hakkin sanin duk abinda ya faru akan wan nan lamarin musammnan a karkashin mulkin Damokaradiyya.

A karshe ya bada shawarar hukumar da za’a kafa ta kunshi harda tsofaffin manyan hafsoshin sojoji domin su gano gaskiyar maganar su bayyanawa ‘yan Najeriya gaskiyar yadda ake yaki da ‘yan ta’adda da kuma yadda za’a kawo karshe shi.

Related stories

Leave a Reply