Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeriya: Anyi Sauye-Sauye A Rundunar Sojoji

army-logo
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumomin soji a kasar nan sun sauyawa wasu manyan hafsoshin soja wuraren ayyukansu.

A yanzu haka dai Laftanar Janar LO Adeosun, shi ne babban jami’in gudanar da tsare-tsare, ya yin da manjo janar AO Shodunke ya zama babban jami’in kula da harkar tsaro a shalkwatar tsaron kasar nan. Shi kuma manjo janar AA Tarfa ya kasance sabon shugaban makarantar horaswa da koyon dabarun harkokin soji dake Minna.

Shi kuwa Gen EO Udoh shi ne babban jami’in dake kula da horarwa da kuma gudanar da ayyukan yau da kullum, Manjo janar MS Yusuf yanzu shi ne babban jami’I mai kula da harkar mulki, ya in da Manjo janar J.I Unuigbe ya zama mai kula da harkokin kayayyakin gudanarwar sojoji. Ya yin da manjo janar Azinta ya kasance babban jami’in kula da inganci da kuma bibiyar ayyukan sojoji.

Hakazalika Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai ya taya su murnar sabobbin mukaman da suka samu kuma ya hore su da dauki ayyukansu da matukar mahimmanci tare da biyayya ga hukumomin soji.

Related stories

Leave a Reply