
anyi ruwan sama mai yawan gaske a nan birnin Maiduguri, daga misalin karfe 8;30 na safe zuwa karfe 1 na rana. Wannan ruwa yasa ba’a bude harkokin kasuwanci ba, wanda aka samu tsaiko a zirga-zirgar ababen hawa.
A yayin da watan Agusta ke matsowa, akwai yiyuwar samun ruwan sama makamancin wannan, domin kuwa ana tsammanin samun damuna mai harshe a inda manoma zasu maida hankali wajen aikin noma domin samar da isasshen abinci.
Yawancin lokutan damuna akan samu ambaliyar ruwa a cikin biranai, shiyasa gidan rediyon Dandal Kura ke kira ga jama’a da su tsabtace magudanan ruwansu.

