Najeriya: An Yankewa Wani Mutum Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Sakamakon Kashe Budurwarsa A JIhar Yobe

Babbar kotun dake jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya ta yankewa wani mai suna Muhammed Adamu hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kashe budurwarsa mai suna Hauwa Muhammad yar shekara 24.

Yayin shari’ar Alkali Justice A. Jauro ya same shi da laifin kisa kakashin sashi na 221 na kundi tsarin shari’ar.

Jauro ya bayyana cewa wanda ake zargin ya kashe Hauwa yana sane ba tare da wani abu ba, ya kara da cewa kotun ta yanke masa wan nan hukuncin karkashin sashi na 273 a kundin shari’ar laifuka.

Yayin da yake Magana da manema labarai bayan yanke shari’ar mai kare wanda ake zargi Mr. M. Dauda yace zai duba shari’ar kuma zasu daukaka kara. Haka nan wanda ake zargin ya bayyana cewa yana addu’a ayi masa hukuncin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *