Najeriya: An Samu Rashin Wutar Lantarki Sakamakon Daukewar Wasu Injina – TCN

By Babagana Bukar Wakil Ngala

Kamfanin da yake bada wutar lantarki a Najeriya wato (TCN) ya bayyana cewa an samu matsalar wutar ne ranar 8 ga watan Mayu da karfeat 2:32 na yamma sakamakon lalacewar wasu kayayyakin wutar wanda yayi sanadiyyar saukar wutar a gurare da dama a jihaohin Onitsha da Anambra da suke kudu maso gabshin Najeriya.

Manajan darakta na kamfanin Mr. Mohammad Usman ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar ranar juma’a a Abuja.

Hukumar ta samu wasu matsalolin ranar laraba wanda suka rage yadda ake samun wutar da ake rabawa kamfanonin bada wutar a kasa baki daya.

Mohammad ya kara da cewa daya daga cikin injinan bada wutar ma ya dauke inda da yawa daga cikin wutar ta sauka, haka nan ya bayyana cewa abinda ya faru shekaranjiya duk sakamakon saukar wutar ne daga yankin bada wuta na onitsha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *