
An kori wasu daga cikin ma’aikatan asibitin Dalhatu Araf Specialist Hospital dake garin Lafia a jihar Nasarawa sakamakon satar jinin da ake bayarwa don marasa lafiya dama sama da fadi da wasu kudade na asibitin.
Shugaban asibitin Dr Hassan Ikrama e ya bayyana hakan yayin da yake hira da manema labarai a garin Lafia.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin su suna satar kudin daga ma’ajiyar jinni ta asibitin suna sayarwa asibitocin kudi kuma suna karkatar da wasu kudade na asibitin.
Ya kara da cewa wasu kuma na amfani da kayayyakin aikin asibitin suna yiwa wasu gwaje-gwaje inda suke saka kudaden a aljihunsu, inda yace su gudanar da bincike kuma duk samu wadanda ake zargin da aikata laifukan.
Ikrama ya kuma bayyana cewa lokacin da aka sa shi a matsayin shugaban asibitin ya gano wasu hanyoyi da dama da ake karkatar da kudade wadanda ya kamata a toshe.
San nan yace mahukuntan asibitin sun gano kalubalen inda zasu kara dakin yin tiyata zuwa 3, dakunan shan magani zuwa 8 sai injin gwaji da suke da guda daya suna so su maida shi 8.
Ya kara da cewa sun karo kayayyakin aiki don karfafa ayyukan asibitin da kula da marasa lafiya don cigaban asibitin. Haka nan ya tabbatarwa al’umma cewa hukumar asibitin zata yi iyakar kokarinta don samar da ayyukan da suka dace.
