Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeriya: An Kama wani Likitan Bogi Dan Kasar Ghana A Jihar Legas

hospital
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Yansandan jihar Legas sun gano wani asibiti da ake gudanar da ayyuka ba bisa ka’ida ba na wani dan kasar Ghana da ya kai shekaru 23 yana gudanar da ayyukansa ba bisa ka’ida ba a unguwar Mafoluku.  

An bayyana cewa mai gudanar da asibitin wanda aka sani da HayforeAdu – Peprah, yazo Najeriya a matsayin malami ta fannin jinya a shekarar inda daga baya ya gina asibitin ba bisa ka’ida ba a shekarar 1982

Asirinshi ya tonu bayan wata mata ta rasa danta bayan ta ziyarci asibitinsa a watan satumba sakamakon kumburin kafa, wanda sakamakon bincike aka gano ba likita bane.

An rawaito cewa mai asibtin ya kasa bada takardunshi ba na samun damar mallakar asibitin .

A inda ya nuna cewa yana fama ciwukan na hawan jini, ciwon suga da ciwon koda.

Related stories

Leave a Reply