Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeriya: An Kama Jami’an Civil Defence 26 Da Sojoji 6 Da Sayarwa Yan Bindiga Makamai

arms
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Muaazu Uamar Hardawa

Jami’an soji da sanannan mafaraucin nan Ali Kwara sun bayyana yadda aka gano jami’an Civil Defence Corps guda 26 da sojoji 6 wadanda aka kama suna sayarwa ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihohin Katsina da Zamfara.

yayin da yake ganawa da manema labarai a Azare, Alhaji Ali Kwara ya kara da cewa an samu nasarar ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin jamia’an tsaron a shirin da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa.

ya kara da cewa an gano hakan ne yayin da ya kama wani dan fashi wanda ya bayyana masa cewa akwai jami’an da suka fishi, inda ya bayyana masa yadda jami’an suke gudanar da munanan ayyukan.

San nan ya tabbatar da cewa tuni kwamandan Civil Defence Corps ya bada umarnin korar jami’an dake da hannnun inda aka mika su kotu.

Alhaji Kwara ya kirayi hukumomin tsaro da su daga da yaki da mugayen laifuka sai kuma kiran da yayi ga gwamnatin tarayya data samarwa matasa ayyukan yi.

Related stories

Leave a Reply