Najeriya: An Danganta Yawan Ciwon Koda Da Shan Magungunan Gargajiya

AMINU KANO TEACHING HOSPITAL
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Babban Darakta mai kula da lafiya na rukon kwarya a asibitin koyarwa na jihar Kano wato Aminu Kano Teaching Hospital Kano, farfesa Abdurrahman Abba Sheshe ya danganta yawan samu ciwon koda da mutane suke samu daga amfani da magungunan gargajiya.

Ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye dalibai na shekarar 2019/2020 na ma’aikatan jinya da aka gudanar ajami’ar ranar. Inda ya yayi kira ga daliban dasu yi kokari su kare kansu.

San nan ya bayyana rashin jin dadinsa na yadda zaka ga mutane musammman mata sun yini a gurin bin layin karbar maganin gargajiya daga masu sayarwa ko don yayansu ba tare da tunanin abunda abin zai haifar ba.

Ya kara da cewa yadda ciwon yake kama yara da matasa abin tashin hankali  ne inda yace akwai bukatar a wayarwa da mutane kai.

A karshen ya taya daliban muranar kamala karatunsu inda ya kirayesu dasu dinga gudanar da ayyukansu yadda ya kamata kuma su tuna zasu koma ga Allah, san nan ya godewa Alhaji  Aminu Alhassan Dantata wanda shine na farko day a fara basu kyautar injin wanke kodar wanda aka fara a shekarar 1999.

Related stories

Leave a Reply