Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeria: ‘Yansanda Sun Mika Sanata Elisha Abbo Gaban Kuliya

elisha Abbo
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Yan sandan Najeriya sun kama Sanata Elisha Abbo inda suka mika shi zuwa kotun magistare dake Zuba a Abuja kan cin zarafi.

Kwamishinan ‘yansandan babban birnin Bala Ciroma ne ya tabbatar da hakan inda yace sun mika Abbo zuwa kotu.

‘yansanda masu bincike sun samar da kafa wani bincike kan sharia’ar ta sanatan dan jam’iyyar PDP wanda yake wakiltar Adamawa ta arewa a majalisar kasar.

A kwanaki ne dai yansandan birnin tarayyar ta Najeriya suka gudanar da bincike kan kan sanatan inda suka tsare shi na awa 24 inda daga baya ya bawa ‘yan Najeriya hakuri kan dukan mata mai shayarwa a shago wanda hakan yasa National Council for Women Society (NCWS) dake Abuja suka mika sunan Sanata Elisha Abbo ga majalisar dinkin duniya.

Related stories

Leave a Reply