
gwamnan babagana zulum yace irin yanayin da kan iyakokin mu suke a kasar nan shi yake azzaba rashin tsaron da muke fa,a da shi.
gwamnan yana wannan bayanin ne a fadar shugaban kasa a Abuja bayan yayi ganawar sirri da shugaban kasa.
yayi nuni da cewa jahar Borno tana iyaka da kasashe kamar su Chadi, jamhuriyyar Niger da kamaru.
gwamnan yace yan ta’addan sun kunshi kabilu iri-iri saboda haka za’a ci gaba Magana da wasu daga cikin su domin su aje makaman su tare da taimakon sarakuna da shuwagabannin addinai.
