
Baza a iya kwatanta rashin Imani da ‘yan kungiyar Boko Haram suke kamantawa ba kamar yadda wasu mata dake yankin Kalagari wanda keda iyaka da Arewacin Kamaru da Najeriya suka bayyana.
A harin da ‘yan kungiyar suka gudanar a kwanakin nan sun cire kunnen matan dake kai rahotonsu ga jami’an tsaron Kamaru da kuma jami’an hadin gwiwa da aka kafa don dakile ta’addanci.
Matan na daga cikin ‘yan kungiyar sa kai dake yankin, haka nan yayin da ‘yan kungiyar suka kawo harin sun fi karfin jami’an tsaron dake yankin. Inda suka kai hari garin su kimanin 300, inda fararen hula 8 suka samu raunuka yayin harin.
Ana nan ana sukar Shugaban kasar Kamaru Paul Biya sakamakon biris da yayi kan harin na Kalagari da Darak. Biya ya aika sakon ta’aziyya zuwa ga takwaranshi na kasar Najeriya Muhammadu Buhari kan harin da aka gudanar a satin daya gabata a Nganzai dake jihar Borno wanda aka kashe kimanin mutane 70.
