Najeriya: Hukumomin Gidan Yari Da kashe Gobara zasu Dauki Mutane Wajen 10,000 Aiki

dambazau 2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar gida yari da ta kashe gobara a Najeriya zasu dauki ma’akata wajen 10,000 a Najeriya inda gidan yari zasu dauki mutane 7, 475, ta kashe gobar kuma zasu dauki sababbib na’aikata 2,200.

Duka ma’aikatun biyu sun samu yarjewa daga Civil Defence, kashe gobara, fasa kauri da gidan yari wanda Ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau ne shugaban su.

Hukumar ta kawo karshen matsalar dake tsakanin mai digiri dame babbar Diploma a daukar ma’aikatan karkashin ma’aikatar cikin gida inji kamfanin dillancin labarai na NAN ranar talata.

Al-Hassan Yakmut ya bayana cewa anyi atro kan lamari amma ba’a fadi yaushe za’a fara daukar ma’aikatan ba kawai sunyi aiki kan dai-daita digiri ne da babbar diploma.

Dambazau yayiwa masu sha’awar aikin fatan alkhairi san nan ya kirayi ma’aikatun dasu tabbatar da sun basu horo na musamman.

Related stories

Leave a Reply