Mutum 41 Sun Rasu A JIrgin Fasinja Na Kasar Rasha Daya Kama Wuta

Wani jirgin saman fasinja na kasar Rasha yayi saukar gaggawa yayin da wuta ta kama a filin saukar jirgin sama na kasar Moscow inda mutane 41 suka rasa rayukansu.

Mutane 37 suka samu raunuka, 5 kuma suna kwance a asibiti. Kwamitin bincike na kasar Rashan ya tabbatar da mutuwar mutanen ciki har da yara 2, Jirgin dai na dauke da fasinjoji 73, ma’aikata 5.

Jirgin ya tashi ne daga kasar Moscow daga yammacin garin Murmansk, dole ya koma saboda matsalar na’ura da aka samu wanda hakan yasa ya kama da wuta.

Wani fasinja daga wani jirgin mai suna Norenko Mikhail ya dauki Faifan bidiyon yadda wuta da bakin hayakin ke fita daga cikin jirgin yayin da yak e kokarin tsayawa.

Masu aikin kashe gobara sunyi kokarin kashe wutar inda tuni aka ci gaba da aiki a filin jirgin saman duk da an soke tashin wasu jiragen.

Shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin ya mika sakon ta’aziyyarsa ga wadanda abun ya shafa, haka nan ya bukaci da a gudanar da cikakken bincikekan yadda wutar ta tashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *