Mutane 55 Sun Rasu Hatsarin Tankar Mai a Nijar

Mahukunta a kasar Nijar sun bayyana cewa kimanin mutane 55 ne suka rasu a hatsarin da wata tankar mai ta kama da wuta kusa da filar saukar jirage a kasar.

Shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya kirayi wan nan lamarin a matsayin abun tashin hankali a kasar bayan ya ziiyarci asibitin da aka kwantar da wadanda suka samu raunukan.

Ana ganin wutar ta tashi sakamakon faduwar tankar kusa da gidan iskar gas station. Mutane da dama sunzo diban man yayin da motar ta fadi wanda hakan ya cefa rayuwar mutane da dama cikin hatsarin.

Irin haka yasha faruwa a yammacin Afirika inda mutane ke jefa kansu cikin hatsari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *