Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Miyetti Allah Ta Bawa Gwamnatin Shawarar Shirya Yarjejniyar Kungiyar Kasashen Yammacin Africa

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi amfani da ka’idar takardar shedar wucewa ta ECOWAS, don duba kwararar makiyaya daga ƙasashe makwabta.

Kiran na kunshe ne a cikin wata sanarwa, wacce shugaban da sakataren sa, Alhaji Muhammad Kiruwa, Alhaji Baba Ngelzarma suka sanya wa hannu.

Ngelzarma, wanda ya bayyana cewa shawarar na cikin shawarwarin da aka cimma a ƙarshen taron zartarwa na ƙungiyar na yini ɗaya tare da Shugaban Kwamitin Amintattu, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, wanda aka gudanar a Abuja.

Ya ce an kira taron ne don yin bitar tabarbarewar yanayin tsaro a kasar, saboda ya shafi membobinta inda ake danganta duk makiyaya masu aikata laifuka ne da ‘yan fashi ta kafofin sada zumunta da kafafen yada labarai.

Ngelzarma ya kuma bayyana cewa taron ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta aiwatar da shirye-shiryen fadakarwa da sake shiryawa ga makiyaya, tare da sake fasalin shirin ilimin makiyaya ga ‘ya’yansu.

Hakazalika, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta magance lamarin kan iyakokin da ba su da yawa, wanda hakan ya ba da damar yawaitar makamai.

Ya yi alkawarin hadin kai da goyan bayan kungiyar ga gwamnatin tarayya da na jihohi, sarakunan gargajiya da hukumomin tsaro, don a yaki da ‘yan fashi da garkuwa da mutane a duk sassan kasar nan, yana mai cewa irin wannan hadin kan zai kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da zaman lafiya mai dorewa.

Leave a Reply