Mayakan Boko Haram Sun Kashe Sojojin Chadi 23

By: Babagana Bukar Wakil

Mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Chadi 23 ata bakin jami’an tsaro inda suka ce yana daya daga cikin hari mafi muni da aka gudanar a kasar ta Chadi.

Sun kai harin da sassafe ranar Juma’a a garin Dangdala kusa da gabar tafkin Chadi inji wasu jami’an tsaro guda 2 da suka fadawa Reuters.

Ana zaton maharani sun tsallaka iyaka ne daga Nijar kafin su kawo harin, sojojin na daga cikin G5 Sahel Force da sojojin Amurka suka bawa horo na musamman don yaki da yan ta’addan na Boko Haram.

Haka nan a kudu maso gabashin Nijar an kashe fararen hula 8 ranar alhamis a wani harin Boko Haram a Karidi dake yankin Gueskerou district.

Gueskerou na yankin Diffa region wanda ke da iyaka da tafkin Chadi kuma shine yafi samun hare-hare a kasar Nijar.

An kashe a kalla jami’an tsaro 16 a harin da suka kai ranar 16 ga watan fabarairu da 9 ga watan Maris inda jami’an tsaron Nijar sukace sun kashe yan ta’addan 33 ranar 12 ga watan Maris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *