
Mataimakin shugaban kasar Najeriya farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci birnin Maiduguri dake Arewa maso gabashin Najeriya ranar Talata don kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar mai barin gado Kashim Shettima ya gudanar.
Ziyarar tashi tazo bayan wata daya da shugaban kasar Muhammadu Buhari yayi inda ya kaddamar da ayyuka da dama wanda gwamnatin jihar ta samar.
Mataimakin shugaban kasar ya kaddamar da ayyuka da dama da gwamnan jihar Kashim Shettima ya samar inda yace ayyukan nada matukar yawan da in ba’a yi wasu ba a yanzu zai kai har ranar da za’a rantsar da sabon gwamna ranar 29 ga watan Mayu ba’a gama ba.
Farfesa Osinbajo ya tabbatar wa da mutanen jihar kokarin gwamnatin su na ganin an sake gina Arewa maso gabas.
