Mataimakin Gwamnan Jihar Borno Da Wasu Manya A Gwamnati Sun Karbi Rigakafin Cutar Corona.

By :Babagana Bukar Wakil Ngala, Maiduguri
Mataimakin gwamnan jihar Borno Alh. Umar Kadafur ya karbi rigakafin cutar corona tare da wasu jami’an gwamnati.

Yayin da yake magana jim kadan bayan karban rigakafin, ya shawarci jama’an gari daga shekara 18 zuwa sama da su karbi allurar rigakafin.

Yace an gama shirin yadda za’a bada rigakafin a sansanin yan gudun hijira da kuma kananan hukumomi.

Ya kuma shawarci jama’a da su cigaba da bin dokoki koda sun karbi rigakafin.

Shugaban ma’aikatan ga gwamna Zulum Isa Marte yace rigakafin zai rage mace mace da kuma kare al’umma daga cututtuka.

An kaddamar da kashi na farko na rigakafin a ranar Alhamis a asibitin Muhammad Shuwa inda aka yiwa ma’aikatan kiwon lafiya 20 rigakafin.

Majalisar dinkin duniya tayi alkawarin samar da helicoptan da zai kai rigakafin zuwa kananan hukumomi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *