Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Masu Saida Man Fetur A Bakin Tituna Suna Cigaba Da Harkokin Su A Maiduguri.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Babagana Bukar Wakil Ngala, Maiduguri
Har yanzau masu sayar da man fetur a bakin tituna na cigaba da sana’ar su a wasu bangare a Maiduguri.

Gidan radiyo Dandal Kura ta rawaito cewa a yanzu an daina samun dogon layi a gidajen mai bayan jita jitan da aka yada na Karin kudin man fetur.

Kamar yadda wakilin mu Babagana Bukar Wakil Ngala ya rawaito, masu sayar da mai sun a harkokin su tsakanin titin Custom zuwa Tashan Bama da Tashan Baga zuwa Bulumkutu kuma ana samun masu siyan yayin da yawancin gidajen man a rufe suke inda ake sai da lita daya tsakanin naira dari 1 da 80, dari 2 da 80 zuwa dari 3.

Wani mai saida man mai suna Umar Hassan yace yana farin ciki da karancin man hakan yana sa ana siyan nashi duk da a yanzu babu dogon layi a gidan man wadan da basa iya jiran layi suna siyan nasu.
Wani mai suna Ibrahim Mubarak ya bayyana cewa ya shiga wannan harkar domin samun abin yi ne.

A nashi bangaran Chiroma Goni mai siyan mai yace har yanzu akwai layi a gidan mai kuma aikin sa bazai barshi ya bi layi ba.

Nwachukwu Ozoku yace wasu gidajen mai basa siyar da mai a yadda farashin take , yayi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su magance lamarin.

Ita kuma Angela Uba tace ta fi son ta siya a gidan mai akan ta siya a wajen mutane akan hanya dan hakan ya sanya ta asara, inda tace tana sa ran komai zai daidai ta nan ba da jimawa ba.

Leave a Reply