Masu Garkuwa Da Mutane Sun Tsare Titin Kaduna Zuwa Abuja

Masu garkuwa da mutane sun kara tsare titin Kaduna zuwa Abuja ranar litinin inda wasu suka gudu suka bar abubuwan hawansu suka shiga daji neman mafaka don kar ayi garkuwa dasu.

Mutane da dama sun gudu ba adadi inda suka bar kayansu masu garkuwar suka zo suka sace. Wani ma’aikacin kamfanin labaran NAN wanda ya tsira da kyar cikin harin ya bayyana cewa abun ya faru kilomita kadan zuwa kauyen Katari dake karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna da misalign 3.30 na yamma.

Dandal Kura sun samu rahoto cewa masu abubuwan hawa sun tare hanya daga titunan guda biyu na fiye da mintuna 40, yan ta’addan sun tafi da wasu mutane daga bisani jam’an tsaro suka ziyarci gurin da abun ya faru kamar yadda wani ya shaida wa wakilin Dandal Kura Babagana ta wayar tarho.

Matafiya sun kirayi jami’an tsaro dasu dinga mafani da kayan fasaha na zamani da jirage masu saukar ungulu don gano masu garkuwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *