
Marubuciyar nan Valeria Porokhova, data fassara Alkur’ani ta rasu tana da shekara 79.
Dan marubuciyar Khalid Al-Roushd, wanda ma’aikaci ne a RT Arabic, ya bayyana rasuwar mahaifiyar ta sa a shafinsa na Facebook.
An haifi Valeria Porokhova a shekarar 1940 inda ta rasu a shekarar 2019. Valeria ta fassara al kura’nin da harshen Rashanci a shekarar 1995.

