Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Manomar Shinkafa Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa A Jihar Adamawa .

rice
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

A Najeriya kungiyar masu nomar shinkafa na kasa reshin jihar Adamawa sun ce tattalin abinci na fuskantar barazana bayan ambaliyar da ta shafi mambobinsu dubu biyar.

Shugaban kungiyar, Maduwa yace a baya suna da mambobi dubu bakwai da sukayi rajista da kungiyar amma kawo yanzu basu kayyade barnar da amballiyar tayi ba, inda yace anasa ran za’a yi girbi mai yawa kafin asarar ya rubanya.

Ya kara da cewa sun samu labarai daga ofishinsu na kananan hukumomi da dama da ambaliyar ya shafa.

Haka zalika yace kananan hukumomin Jada, Ganye da Tongo sune suka tsira cikin kananan hukumomi 21 na jihar da ambaliyar ya yiwa ta’adi.

Har ila yau ya ce galibin manoman sunyi amfani da bashin bankuna yayin nomar damunan inda ya nemi gwamnati data shiga al’amarinsu domin taimaka musu.

Anasa bangaren Dr Muhammed Suleiman shugaban agajin gaggawa na jihar wato SEMA yace sun fara bincike kan wuraren da abin ya shafa.

Related stories

Leave a Reply