Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Makarantun Poly A Najeriya Zasu Fara Yajin Aiki

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar makarantun Poly sunyi barazanar fara yajin aiki daga 6 ga watan Afrilu mai kamawa a duk fadin kasa bisa abinda ta misalta da lamari da gwamnatin tarayya bata sasanta ba a wasu jihohi.

Kungiyar tayi jan hanakalin ne cikin bayanin bayan taro na karo 99 da majalisar kungiyar tayi ranar Juma’a daya gabata a jihar Katsina.

Shugaban ASUP, Mr Anderson Ezeibe shi ya rattaba hannu kan bayanin kuma yace kungiyar ta dauki matakin ne domin taja hankalin gwamnati kan bukatar sake kudin bashin watanni 10 daya kamata a biya mambobinta karkashin sabon tsarin biyan albashi tare da cewa baya ga hakan akwai bukatar sake duba shugabancin makarantu na tarayya dama jihohi baki daya.

Haka zalika kungiyar ta bukaci gwamnati ta gyara makarantun jihohin Adamawa, Kano, Sokoto, Abia, Niger da sauran jihohi, sa’annan suka nemi biyan albashin ma’aikata a jihohin Abia, Ogun, Osun, Benue, Plateau, Edo da Cross Rivers kuma suka nemi ayi amfani da tsarin biyan albashin a jihohin Sokoto, Kaduna, Adamawa da sauran su.

Har ila yau Cikin bayanan, kungiyar ta bukaci gwamnatocin jihohin Kano da Kaduna dasu yi amfani da dokar barin aiki a sheakaru 65 a makarantun su

Leave a Reply