MAHAJJATA DA DAMA SUNKOMA GIDA NAJERIYA DAGA KASA MAI SARKI

Hukumar Mahajjatan Najeriya tace a ranar litinin mahajjata dubu sha uku da dari biyu da ashirin da uku sun dawo daga kasa mai tsarki wato Saudi Arabia.

Acewar hukumar hajjin Najeriya dake kasar Saudi Arabia mahajjatan jihar Yobe guda 315 sunbi jirgin  Medview daga birnin Jedda zuwa filin sauka da tashi na jihar Borno.

Hukumar mahajjatan ta kara da cewa jiragen Medview da Max Air sun dawo da mahajjata 509 na jihohin Kaduna, Enugu da kuma Filato.

Sama da mahajjata 50, 000 daga kasar Najeriya ne suka samu yin aikin Hajji a wannan shekarar.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *