
Hafsan sojin kasa Lt Gen Ibrahim Attahiru ya kai ziyara hedikawatan runduna na 6 a patacol, inda ya bukaci jami’ai da soji dasuyi aiki tare da hangen nesa na rundunar sojojin Najeriyar wajen nuna dukkan korewa domin cin galaba kan makiyan a koda yaushe.
Yayin ziyarar, hafsan ya samu rakiyar komandan runduna na 6 da kuma komandan Operation Delta Safe, Maj General Sanni Gambo Mohammed inda samu tarbar na musamman bisa halaccin wasu runduna na sama, daraktoci, yan sanda da sauran su.
Hafsan sojin ya sake tuni game da muradun sa na ksasncewa cikin shiri ko wani lokuta, da bada cikakken amincewa ga shugaban kasa baki daya da kuma aiki da dokoki da tanade-tanaden aikin soji.

Daya ziyarci bataliya ta 29 na OPERATION DELTA SAFE a barikin na patakol.
ya basu tabbacin cewa a shirye yake ya magance matsalolin su cikin kankanin lokaci kuma ya bukaci su dasu kasance masu gaskiya, da nuna korewa yayin aiki inda ya yabawa runduna masu kokari tare da cewa baza’ayi kasa a gwiwa wajen hukunta masu aikata laifi ba kuma yayi kira garesu dasu guji aikata laifi.
