Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Kwamitin zartarwa na fadar shugaban kasa ya amince da Naira miliyan 995 na gyaran tituna

buhari in borno
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kwamitin zartarwa na majalisar fadar shugaban kasa sun amince da fitar da Naira miliyan 995 don gyaran tituna da kuma sayan kayan fasaha da sadarwa na zamani da zasu karfafa hanyoyin kasar

Ministan ayyuka da gidajen Babatunde Fashola ne ya bayyananhakan ga manema labarai dake fadar shugaban kasa a Abuja bayan taron da sukayi a karshen taron da suka gudanar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Acewarsa Naira miliyan 203 za’a kashe wajen sayan kayan samun bayanai da sadarwa inda ragowar naira miliyan 792 za’a kashe wajen gyaran tituna a jihar Zamfara.

Ma’aikatar yada labara ice zata samar da kayan sadarwar da samun bayanai ta yadda zau karfafa da kula da ayyukan mma’aikatar da kuma kula da titunan.

Haka nan miistan yace amfani da kayan kimiyyar zai saka a samu karfafa wajen duba titunan kasar da ginasu dama gyaransu.

A nashi jawabin ministan yada labarai da aladu Alhaji Lai Mohammed yace majalisar zartaswar ta amince da Naira sama da biliyan daya don saka hasken rana na Solar don haskaka tituna da kuma titin Kershi-Jikwoyi dake Abuja.

Leave a Reply