
Kwamitin Sanatocin Najeriya kan rage radadin talauci sun komar da Ministan kula da jama’a, ibtila’I da cigaban mutane Hajia Sa’adiya Umar Faruq kan kasafin kudi.
A cewar shugaban kwamitin Sen. Lawan Yahaya Gumau ma’aikatar tata bata bada yadda zata gudanar da shirye-shiryenta na 2019 ba.
Gumau yace kwamitin bazai yadda da rashin da’a na wasu masu bawa shugaban kasa shawara ba, wadanda suka raka ministar kare kasafin, inda yace dole a kawo kasafin kafin 2020.
San nan ya kirayi ministar data data kawo duk takardun kudaden gaban kwamitin kafin lokacin da suka bata.
A nata jawabin, ministan taba kwamitin hakuri kan rashin kawo takardun kasafin kudin na shekarar 2019 kuma takardun kasafin 2020 data bayar na dauke da flash na kasafin 2019.
