Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Kwamishinan kiddidiga Ta Jihar Yobe Yace Sunyi Nasarori Da Dama Kan Aikin Kidaye Da Kiddidiga A Jihar Yobe.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

y:Hamisu Ado Nguru, Yobe. Kwamishinan Ma’aikatar kidaye da kiddidiga ta jihar yobe, mai-aliyu mohammed, ya bayyana cewar ofishinan sunyi nasarori da dama kan aikin kidaye da kiddidiga a jihar.

Ya bayyana haka a dapchi dake karamar hukumar busari a jihar.Ya bayyana kananan hukumomin daza’a gabatar da ayyukan kamar haka damaturu, potiskum, bade, nguru, machina, yusufari, karasuwa, tarmuwa da fune.

Kwamishinan yace unguwanni uku ne kadai aka ware a karamar hukumar tarmuwa saboda matsalar rashin tsaro da’ake fama da shi, tareda yin bayanin cewa ma’aikatar da gwamnatin tareda jami’an tsaro zasuyi kokarin cewar an kaddamar da shirin a yankunan.

Mohammad yace, aikin kirgen da lambobin yana gudana a halin yanzu a karamar hukumar busari da jakusko har 3 ga watan afrilu, wanda zai cigaba a karamar hukumar nengere da fikaYace aikin na kirgen da lambobin gidajen na gudana tareda hadin gwiwar hukumar zabe mai zaman kanta na kasa.

Muhammad ya yabawa kananan hukumomin wajen yadda suka bada hadin kai ga ma’aikatan sa domin samun nasarar aikinShugaban ma’aikatar Alhaji Abdullahi Garba, ya tabbatar wa kwamishinan cewa zasu cigaba da basu hadin kai dan ganin an ankammala ayyukan cikin lafiya da nasara.

Leave a Reply