Kwamandan operation hadin kai ya bukaci karin hadin kai tare da hukumar kiyaye hadurra a jihar Borno.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kwamandan Operation Hadin Kai manjo janar Christopher Musa, ya yi kira da a kara hada kai da hukumar kiyaye haddura ta kasa da sauran masu ruwa da tsaki a yakin da ake yi da yan ta’adda.

Manjo janar Musa ya yi wannan kiran ne a Maiduguri lokacin da ya kai ziyarar fahimtar juna a shalkwatan rundunar ta FRSC da ke jihar Borno.

Ya ce hukumar ta FRSC a Borno tana aiki tare da sojoji kuma ana bukatar ci gaba da aikin ta hanyoyin ta na musamman.

A cewarsa Operation hadin kai wanda ke yin aiki tare cikin harshen Hausa, yana jaddada buƙatar kowa da kowa ya haɗa hannu waje guda don tabbatar da kawo ƙarshen yan ta’adda.

Kwamandan ya lura cewa mika wuyan da yan kungiyar Boko Haram suka yi a halin yanzu ya sa dole ya yaba da kokin hukumar wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kan hanyoyin jihar tare da tabbatar da taimakon sojoji don inganta ayyukan su a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Da yake mayar da martani, kwamandan sashin hukumar ta jihar, Mr. Sanusi lbrahim ya yabawa kwamandan saboda jajircewarsa na ci gaba da haɗin gwiwa tare da hukumar tare da ba shi tabbacin ci gaba da ba da goyon baya.

Leave a Reply