Nijeriya: Kungiyar yan Jaridu Ta Kasa Zata Mika Kudiri Kan Kafofin Yada Labarai Da Basa Biyan Ma’aikatansu

NUJ
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar yan jaridu ta kasa da hadin gwiwar masu buga jaridu sunce zasu fara shirya yadda mika kudirin da zai kirkiro dokar hukunta kamfanin watsa labarai da ma’aikatakansu ke binsu bashi.

Shugaban kungiyar Christopher Isiguzo ne ya bayyana hakan a Makurdi, dake jihar Benue yayin tattaunawa da yayi da mambobin kungiyar jihar don ya gode musu kan zabensa da sukayi kuma don yasan kalubalen da suke fuskanta.

Mr Isiguzo yace idan aka maida kudirin doka, kafafen yada labarai zasu dinga biyan ma’aikatansu hakkokinsu kuma masu ruwa da tsakin zasu fara mutunta yan jaridar.

Haka nan yace ana ganin yan jarida a Najeriya a matsayin masu laifi inda ba’a mutunta aikin nasu, don haka kungiyar zatayi kokarin ganin ta hada kan kafafen yada labarai musamman na kafafen sada zumunta don yi musu garambawul.

San nan yace tuni suka bayyanawa shugaba Muhammadu Buhari, shugaban gwamnonin Najeriya, Mr Kayode Fayemi and da ragowar gwamnonin kan yadda ake cin zarafin mabobinsu.

A nata jawabin, Victoria Ashar, shugabar kungiyar a jihar Benue ta yabawa shugaban kungiyar kan wan nan ziyarar inda tace zasu cigaba da bashi hadin kai. SBM/NAN/BBW   BBW     RGK/HAM/BBW

Related stories

Leave a Reply